Labarai

Babbar Kotu Ta Bayar Da Umarnin Korar Sanusi Lamido Daga Fada

Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta bayar da umarnin kori Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II daga fadar Gidan Rumfa da aka mayar. Kotun ta kuma umurci ‘yan sanda da su tabbatar an ba shi duk wani hakki da alfarma na Sarkin Kano na 15, Aminu Bayero.

Kamar yadda Daily Post ta ruwaito, alkalin kotun mai shari’a S. A. Amobeda ne ya bayar da wannan umarni a ranar Talata, inda ya jaddada cewa ya zama wajibi a tabbatar da adalci da zaman lafiya a Kano.

Umurnin dai ya hada da tanade-tanade na hana cin zarafi, ko tsoma baki a kan hakkin Sarkin har sai an ci gaba da shari’a, da kuma ci gaba da shiga gidansa da fadarsa da ke fadar Sarkin Kofar Kudu.

An dage sauraron karar zuwa ranar 4 ga watan Yuni, 2024, domin sauraren karar.

Hakan na zuwa ne jim kadan bayan wata babbar kotun jihar karkashin jagorancin mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta bayar da umarnin hana korar Sarki Sanusi II.