Labarai

Babban Hafsan Sojojin Najeriya Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja Ya Rasu

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, babban kwamandan sojojin kasa, ya sanar da rasuwar Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja, babban hafsan sojin kasa.

Lagbaja ya rasu yana da shekaru 56 a duniya.

A cewar wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya fitar, ya rasu ne a daren ranar Talata a Legas bayan ya yi fama da rashin lafiya.

“An haifi Laftanar Janar Lagbaja a ranar 28 ga Fabrairu, 1968, a ranar 19 ga Yuni, 2023, Shugaba Tinubu ya dora kan muƙamin.

“Babban aikinsa na soja ya fara ne a lokacin da ya shiga makarantar horas da sojoji ta Najeriya a shekarar 1987. A ranar 19 ga Satumba, 1992, aka ba shi mukamin Laftanar na biyu a rundunar sojojin Najeriya a matsayin mamba na kwas na 39 na yau da kullun.

“A tsawon aikinsa, Laftanar Janar Lagbaja ya nuna kyakkyawan jagoranci da jajircewa, inda ya yi aiki a matsayin kwamandan runduna ta 93 da kuma bataliya ta 72 na musamman.

“Ya taka rawar gani sosai a ayyukan tsaron cikin gida da dama da suka hada da Operation ZAKI a jihar Binuwai, Lafiya Dole a Borno, Udoka a Kudu maso Gabashin Najeriya, da Operation Forest Sanity a fadin jihar Kaduna da Neja.

“Wani tsohon dalibin babbar jami’ar Yakin Sojojin Amurka, ya samu digirin digirgir a fannin Dabarun Dabaru, inda ya nuna kwazonsa ga ci gaban aiki da kwazonsa a shugabancin soja.

“Lt. Janar Lagbaja ya rasu ya bar matar sa Mariya da ‘ya’yansu biyu.

“Shugaba Tinubu ya jajantawa iyalansa da sojojin Najeriya a wannan mawuyacin lokaci. Ya kuma yi wa Laftanar Janar Lagbaja fatan alheri tare da girmama gagarumar gudunmawar da yake baiwa al’ummar kasar,” sanarwar ta kara da cewa.

Advertisement