Labarai
An Yanke Wa Tsohon Shugaban Ƙasa Hukuncin Daurin Rai-Da-Rai
Wata kotu a kasar Burkina Faso ta yanke wa tsohon shugaban kasar Blaise Compaore hukuncin daurin rai da rai bisa samun shi da laifin kashe magabacin shi, Thomas Sankara.
Hukuncin da aka dade ana jira a ranar Laraba ya kawo karshen shari’ar da aka shafe watanni shida ana yi kan kisan Sankara, wanda aka kashe a lokacin juyin mulkin da abokin shi Compaoré ya jagoranta a ranar 15 ga Oktoba, 1987.