Labarai

Amarya Ƴar Shekara 20 Ta Kashe Uwar-Gida Mai Shekaru 32 Da Taɓarya

Wata mata ta biyu mai shekaru 20 a duniya a halin yanzu jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi na cigaba da yi mata tambayoyi bayan da ta yi amfani da wata taɓarya ta bugi matar mijinta ta farko a kai a lokacin da take barci, lamarin da yayi sanadin mutuwar ta. Hukumar ta sanar a ranar Litinin, 28 ga Nuwamba.

An kama matar ta biyu (Amarya) mai suna Maryam Ibrahim bayan mijinta mai suna Sambo Ibrahim ya kai rahoton faruwar lamarin a ofishin ‘yan sanda na Maina-Maji.

A cewar rahoton da mutumin ya shigar, matar shi ​​ta biyu dauke da tabarya, ta shiga dakin matar shi ta farko, mai suna Hafsat Ibrahim, mai shekaru 32, inda ya buge ta a kai, lamarin da yayi sanadin mutuwar ta saboda samun raunuka.

An ce an garzaya da matar ta farko wani asibiti a yankin inda likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da rasuwar ta.

Kamar yadda wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar ta fitar ta hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Ahmed Muhammad Wakil, kuma ta wallafa a bangon shafin facebook na rundunar a ranar Litinin, yayin da ake yi mata tambayoyi, an ce matar ta amsa laifin ta ne saboda fushi.

Rahoton yace, matar ta farko ta aiko da danta ya ba matar ta biyu soyayyen nama, amma bayan ta ci naman, sai ta ji ba dadi, sai ta fara amai.

Jin cewa amai nata na iya faruwa ne sakamakon ciwon Ulcer da take fama da shi, sai aka ce matar kanin mijinta ta ba ta maganin ulcer amma matar ta fusata. Bayan haka, ta tafi kicin dinta, ta dauko tabarya, ta shiga dakin matar farko a lokacin da take barci ta buge ta a kai.

A halin yanzu tana ba da ƙarin bayani ga jami’an ‘yan sanda bayan haka ana sa ran za a gurfanar da ita a gaban kotu don gurfanar da ita.