Labarai

Abinda Masana Suka Gano Karkashin Teku Da Ya Bai Wa Duniya Mamaki

Shekaru da yawa koguna, Tafkuna da Tekuna ana ganin su zaman abubuwan halittae Ubangiji masu ban sha’awa. An gudanar da bincike da yawa akan wadannan ruwayoyin amma har yanzu masana kimiyya suna mamakin binciken da suke yi a kowace rana.

Wasu daga cikin abubuwan da suka fi ban mamaki da aka gano a ƙarƙashin ruwa sun haɗa da ragowar shekaru 13,000 na mafarauci na ɗan asalin Amurka da kuma birni mai tsarki na karkashin ruwa.

A cikin wannan labarin za mu kalli wani abin gaskiya na baya-bayan nan wanda ya bai wa duniya mamaki. Wani mai nutsewa yayin da yake cikin teku ya gano wasu sassaken mutane a kasan tekun wadanda ke lankwashe da kawunan su a cikin yashin Tekun, kamar suna (Sujada) a sallah.

Wadannan sassake-sassake sun baiwa masana kimiyya mamaki domin sun kasa bayyana ma’anar sassaken. Amma kamar yadda muke gani, kamar suna yin (Sujuda) irin ta musulmai masu yin sallah.

An gabatar da bayanai daban-daban don bayyana dalilin da yasa aka samu sassaken a cikin teku. Wasu dai sun ce masu sana’ar dinki na Jason ne suka dora su domin wayar da kan duniya illar da ke tattare da sauyin yanayi da kuma tura mutane don kare teku.

https://youtu.be/qrhA_NOUhbI