Labarai

Abdullahi Sani Abacha Ya Rasu

Abdullahi Sani Abacha, dan marigayi shugaban mulkin sojan Najeriya, Sani Abacha, ya rasu.

Uwargidan sa Fatimah Gumsu Abacha-Buni, wacce ita ce uwargidan gwamnan jihar Yobe, ta bayyana hakan a ranar Asabar ta shafinta na Instagram da aka tabbatar.

Ya rasu ne a cikin barcinsa, a gidan iyalin da ke titin Nelson Mandela, Abuja.

Ta rubuta: “Innalillahi wa inna ilaihi rajiun (Lallai mu na Allah ne, kuma gare shi muke komawa). Na rasa kanina Abdullahi Sani Abacha. Ya mutu a cikin barcinsa. Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma sanya masa jannatul firdaus (aljannah) Amin. Don Allah ku sanya shi a cikin addu’o’inku”.

Za’ayi Sallar Jana’izar a babban Masallacin kasa dake Abuja da karfe 4 na yamma.

Marigayin na daya daga cikin ‘ya’yan tsohon shugaban kasa tara.