Kasuwanci

1973: Hotunan Pound Na Najeriya Kafin A Fara Amfani Da Naira

Kafin shigar da Naira a matsayin hanyar musanya, fam din Najeriya shi ne kudin da ake amfani da shi tsakanin shekarun 1907 zuwa 1973. Sai dai Najeriya ta yi amfani da Fam na Afirka ta Yamma, kafin ta fitar da nata fam din.

Fam na Najeriya, wanda yayi daidai da fam na Burtaniya, kuma ba shi da wata wahala wajen musayar kudaden kasashen biyu.

Daga baya an maye gurbin fam din tare da shigar da kudin Najeriya naira a shekarar 1973, a kan canjin fam 1 na kasar Ingila, daidai da naira 2 na Najeriya.

Wannan canji ya faru ne a cikin 1973, ya sanya Najeriya ta zama kasa ta karshe da ta yi watsi da tsarin kudin £ sd (sunan da aka fi sani da pre-decimal Currencies wanda ya zama ruwan dare a duk Turai).