Wasanni

Ɗan Kwallon Farko Da Ya Taɓa Cin Ƙwallo Da Bugun Kwana

Cesareo Onzari na Argentina shi ne kwararren dan wasan kwallon kafa na farko da ya ci kwallo kai tsaye daga bugun kusurwa.

Hakan ya faru ne a lokacin wasan sada zumunci tsakanin Uruguay da Argentina a Estadio Sportivo Baracas a ranar 2 ga Oktoban 1924. Wasan ya samu halartar ‘yan kallo kusan 52,000.