Labarai

Ɗan Ƙasar Faransa, Nabil Ennasri Da Ya Tafi Hajji Akan Keke

Nabil Ennasri mai shekaru 41, ya fara tafiya a birnin Paris a ranar 22 ga Afrilu, kuma ya ketare kasashe 11 da suka hada da Italiya, Slovenia, Croatia, Montenegro, Bosnia da Herzegovina, Albania, Girka, Jordan da Turkiyya.

Alhamdulillah, Nabil Ennasri ya samu yin aikin hajjin wannan shekara, 2023 cikin koshin lafiya.