Labarai

Isra’ila Ta Zargi Falasɗinawa Da Lalata Ƙabarin Annabi Yusuf A.S

Mahukunta a kasar Isra’ila sun ce Falasdinawa sun lalata wani wuri mai tsarki na Yahudawa a Nablus, a yayin da rikici ke ƙara daukar wani sabon salo a tsakanin daɗaɗɗun makiaya biyu, Falasdinawa da dakarun Isra’ila a yankin gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye, wanda aka sha kai ruwa rana akan wannan batun.

Wani shafin Twitter na gwamnatin kasar Isra’ila ya wallafa wani bidiyo da yace ke nuna yadda Falasdinawa ke kai hari a wurin da Yahudawa ke ganin ya ƙunshi ƙabarin Annabi Yusuf, (Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi).

Zuwa yanzu babu wani martani daga ɓangaren Falasdinawa game sa wannan ikirari na Isra’ila kan lalata kabarin na Annabi Yusuf (AS).

Yahudawa na girmama wurin da ƙabarin yake sosai, amma yana cikin yankin Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye na Falasdinawa.

An sha yin artabu lokuta daban daban a wurin, har ta kai aka ƙona wurin kafin aka sake gyara shi.

Ministan tsaron kasar Isra’ila Benny Gantz ya bayyana al’amarin a matsayin “babban laifin saɓawa ƴancin ibada na mutane.”