Labarai

MTN, Airtel Da Sauransu Sun Yi Kiran A Kara Kuɗin Data Da Kira

Shugaban kungiyar Kamfanonin Sadarwa na Najeriya (ALTON), Gbenga Adebayo, ya yi kira da a sake duba farashin ayyukan kamfanonin sadarwa.

ALTON ita ce ƙungiyar kamfanonin sadarwa; MTN Nigeria, Airtel, Globacom, 9mobile da Spectranet, da dai sauransu.

Adebayo, yayin bikin baje kolin abubuwan da suka shafi ‘yan asalin kasar ta Najeriya (NTICE 2023) da aka kammala a ranar Alhamis, ya ce farashin kira da data a halin yanzu sun yi kasa da farashin samar da kamfanonin sadarwa ke kashewa.

“Dole ne mu kalli farashi mai inganci don ayyukan da muke bayarwa saboda farashin yanzu ba ya dorewa. Muna bayar da farashi kasa da farashin samarwar da abubuwan a bangaren mu,” in ji Adebayo.

A halin da ake ciki, shugaban kungiyar ta telco ya kuma ce bankunan ajiyar kudi (DMBs) sun ki biyan basussukan Naira biliyan 150 da suka taso daga amfani da Unstructured Supplementary Service Data (USSD) da abokan huldar bankunan suka yi.

Adebayo ya ce tsoma bakin siyasa ya hana masu samar da hanyar sadarwar daukar mataki. Ya yi imanin cewa ya kamata a toshe damar shiga dandalin USSD tun da bankunan sun kasa cika wajibcinsu na kwangila.

Duk da shiga tsakani da ma’aikatar sadarwa da hukumar sadarwa ta Najeriya NCC da babban bankin Najeriya (CBN) suka yi, har yanzu babu wata hanyar da za a bi.