Tsaro

Zelensky yace Ukraine ba zata shiga kungiyar NATO ba

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ya ce kamata ya yi Ukraine ta amince da cewa ba za ta zama mamba a kungiyar tsaro ta NATO ba.

Advertisement

Yayin wata ganawa da ya yi da shugabannin sojojin kasar, Zelensky ya ce Ukraine ba mamba ce ta NATO, kuma duk da cewa kofofin a bude suke na shiga kungiyar, sun ji cewa ba za su iya shiga ba. Ya yi nuni da cewa haka ita ce gaskiya, kuma dole ne a gane ta.

Lura da cewa Ukraine ta shiga cikin kungiyar tsaro ta NATO, kawancen soji da Amurka ke jagoranta, Rasha ta yi amfani da shi a matsayin hujja kan mamayewar da ta yi a Ukraine ba tare da wani dalili ba.

Advertisement

Advertisement