Zan Tabbatar Da Hana Kafa Ƙasar Falasɗinu – Benjamin Netanyahu
Netanyahu ya ce zai gabatar da doka don yin watsi da kiraye-kirayen neman kafa kasar Falasdinu.
Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya fada a cikin wata sanarwa ta faifan bidiyo cewa zai gabatar da doka ga majalisar Isra’ila ta yin watsi da “kokarin da kasashen duniya ke yi na tilasta kafa kasar Falasdinu” a daidai lokacin da ake ci gaba da kiraye-kirayen samar da kasashe biyu, Isra’ila da Falasdinu.
Matakin dai ya biyo bayan amincewa da matakin da aka dauka baki daya a matakin majalisar ministocin kasar a kwanan baya. Netanyahu ya kuma sake nanata cewa Isra’ila za ta ci gaba da “cikakken kula da tsaro” a yankin Yammacin Kogin Jordan da Gaza da ta mamaye bayan yakin Gaza.
“Tsawon watanni biyar muna gudanar da yaki wanda ba a taba ganin irinsa ba,” in ji jaridar Times of Israel. “Wannan yaƙin ya bai wa mayakan mu yancin yin aiki don cimma dukkan manufofin yaƙi.” Inji Netanyahu.