Siyasa

Zan Lashe Zaɓen Da Goyon Bayan Gwamnonin APC 22 Da Na Shugaban Ƙasa Buhari

Gabanin zaben shugaban kasa na 2023, tsohon gwamnan jihar Legas kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya bayyana dalilin da yasa zai iya yin nasara a zaben 2023. A cewar shi, saboda Jihohi 22 a karkashin Jam’iyyar APC da kuma goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari, zan ci zabe

Ya bayyana hakan ne ta bakin Daraktan Yada Labarai na Majalisar Yakin Neman Zaben Shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bayo Onanuga, yayin da yake mayar da martani ga Lawal kan cewa ba zai iya lashe zaben shugaban kasa a 2023 da tikitin Musulmi da Musulmi ba.

Idan za a iya tunawa, tsohon sakataren gwamnatin tarayya kuma jigo a jam’iyyar APC mai mulki, Mista Babachir Lawan, yace jam’iyyar ba za ta ci zaben shugaban kasa a 2023 ba sakamakon tikitin addini daya.

Advertisement

A hirar shi da BBC, Babachir yace shi da wasu sun goyi bayan Tinubu, don ya ci zaben fidda gwani, amma daga baya suka gane cewa ya boye matakin da ya dauka na zabar musulmi.

Yayin da yake mayar da martani, kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bayo Onanuga yace kalaman Lawal abin dariya ne. Asiwaju bai taba shiga zabe ba kuma ya fadi zabe.

”Jihohi 22 ne ke karkashin APC, tare da goyon bayan shugaban kasa mai ci, A Tinubu na shirin samun gagarumin rinjaye. A bar Babachir ya fara tunkarar rarrabuwar kawuna a kungiyar shi ta ‘yan tawaye, maimakon ya fadi sakamakon zaben.

Advertisement