Zamu Zo Kan Ku: Hafsan Sojojin Najeriya Ya Gargadi Masu Kiran Ayi Juyin Mulki
Babban hafsan hafsoshin tsaron kasar, CDS, Janar Christopher Musa, ya gargadi wadanda ya bayyana a matsayin “miyagu” da ke kira da a yi juyin mulki a Najeriya saboda tabarbarewar tattalin arziki da kasar ke fuskanta.
Musa ya yi gargadin cewa doka za ta zo ga masu kira da a yi juyin mulki a kasar saboda yanayin tattalin arzikin da ake ciki.
Ya yi magana ne bayan kaddamar da babbar kofar shiga runduna ta 6, sojojin Najeriya da jami’an Transit Accommodation, a hedikwatar shiyya da ke Fatakwal, jihar Ribas.
Shugaban rundunar sojin ya tabbatar da aniyar rundunar sojin na tabbatar da dorewar dimokradiyya a Najeriya.
Musa ya ce: “Duk wanda ke yin wannan kira (juyin mulki) baya kaunar Najeriya. Muna so mu bayyana a fili cewa Sojojin Najeriya sun zo ne domin kare dimokradiyya.
“Dukkan mu muna son dimokuradiyya kuma muna yin aiki mai kyau a karkashin dimokuradiyya. Don haka za mu ci gaba da goyon bayan dimokuradiyya. Kuma duk wanda ke kira ga wani abu banda dimokuradiyya miyagu ne kuma ina ganin ba su da wani alheri ga Najeriya.
“Kuma su yi taka tsantsan domin doka za ta biyo bayansu. Muna iya ganin cewa da dimokuradiyya abubuwa da yawa suna faruwa a Najeriya. Eh muna cikin lokutan gwaji, ina nufin a rayuwa babu abin da ya kai kashi dari.”
Musa ya ce Gwamnatin Tarayya ta mayar da hankali wajen magance matsalolin tattalin arzikin da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu don haka ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi hakuri.
“Kowa yana cikin wani yanayi na gwaji a rayuwa, kuma shine abin da kuke yi da su. Za ka ga gwamnati ta yi kokarin ganin mun fito da kyau.
“Kuma idan kun shiga cikin wahalhalu kuma ku fito da kyau za ku yaba da gaske abin da ake gina al’umma.
“Don haka muna cikin lokacin gwaji, amma ina tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za ta samu sauki,” in ji shi.