Zaftarewar Ƙasa Ta Kashe Sama Da Mutane 257 A Ƙasar Habasha
Adadin wadanda suka mutu sakamakon zaftarewar kasa a kasar Habasha, Ethiopia ya kai 257, amma ana sa ran adadin wadanda suka mutu na karshe zai iya kai mutum 500, a cewar ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD OCHA.
Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da alkaluman ne a ranar Alhamis bayan zabtarewar kasa a yankin tsaunukan Gofa da ke kudancin kasar Habasha, wanda ruwan sama na farko ya afku a ranar Litinin, na biyu kuma ya lakume wadanda suka taru domin ceto mutane.
Adadin wadanda suka mutu da aka sake fasalin ya karu da 28 bisa alkaluman da Hukumar Kula da Hadari da Bala’i ta Kasar Habasha ta bayar a ranar Talata.
Daruruwan mutane ne suka shiga cikin jajayen laka a wurin da bala’in ya afku a yankin Kencho Shacha, inda suke neman wadanda suka tsira daga zaftarewar kasa mafi muni da aka samu a kasa ta biyu mafi yawan jama’a a Afirka.
“Fiye da mutane 15,000 ne da abin ya shafa na bukatar a kwashe su daga yankin,” in ji OCHA. Alkaluman sun hada da akalla yara 1,320 da mata masu juna biyu 5,293 da kuma sabbin iyaye mata.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na EBC cewa, an binne akasarin wadanda aka zaftarewar kasr ta afkawa ne bayan da suka je taimakawa mazauna wani gida da kasa ta rufta akan su.
“Wadanda suka yi gaggawar yin aikin ceton rai sun mutu a cikin bala’in, wadanda suka hada da shugaban karamar hukumar, malamai, kwararrun kiwon lafiya da kuma kwararrun aikin gona,” in ji wani jami’in yankin Dagemawi Ayele na cewa.