Siyasa

Zaɓen Gambia: Barrow yayi alkawarin samar da tituna 1200km, zai kawo karshen shigo da shinkafa

Yayin da Shugaban ƙasar Gambia Alhaji Adama Barrow ke ci gaba da yakin neman zabensa a yankin Upper River (URR), ya yi wa magoya bayansa alkawarin gina tituna mai tsawon kilomita 1200 tare da kawo karshen shigo da shinkafa idan aka sake zaben shi a karo na biyu.

Ya kuma yi alkawarin inganta da samar da wutar lantarki a gonakin shinkafa a fadin kasar nan domin magance tashin farashin shinkafa a kasuwa.

A yayin da yake fuskantar dandazon jama’arsa na Basse, shugaba Barrow ya fara jawabinsa ne da jinjinawa magoya bayan Basse NPP da suka rasa rayukansu a kan hanyarsu ta zuwa shaida ranar zaben sa.

Ya bayyana cewa Basse, URR musamman yana da mataimakin shugaban kasa da kuma mukaman ministoci da yawa tun da ya hau mulki, ya kara da cewa Basse ya sha banban da na baya.

“Na gina gadoji na Basse, tituna, makarantar Koba Kunda, kuma na yi hakan a cikin shekaru hudu na kan mulki.” Da yake magana kan zaman lafiya, ya ce “akwai zaman lafiya a kasar nan kuma shi ya sa za mu iya yin rijistar wadannan ci gaban.”

Barrow ya kuma bayyana cewa akwai dimokuradiyya a kasar nan, tare da sauran kasashen Afirka na kokarin bin matakan da ya dauka.

“Idan aka sake zabe ni a ofis, zan gina tituna mai tsawon kilomita 1200. Zan karfafa noman shinkafa kuma in daina shigo da shinkafa daga waje. Hakan zai faru ne idan aka zabe ni kan mulki na tsawon shekaru biyar masu zuwa. Hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan yi da rage farashin kasuwa.”

Ya kuma yi alkawarin kafa masana’antu domin matasa su tsunduma kansu cikin wani abu mai ma’ana.

A ranar 24 ga wannan wata, ya kuma yi alkawarin hada wutar lantarki ta Basse zuwa kasar Senegal kuma za su ci gajiyar wutar na sa’o’i 24.

“A cikin watan Disamba, zan gudanar da tashar samar da wutar lantarki ta Brikama OMVG sannan kuma kamfanin na Soma zai fara aiki. Zan kula da cibiyoyin lafiya 24 tare da wadata dukkan asibitoci da likitoci.”

Advertisement