Siyasa

Zaɓen 2023: Tinubu ya dawo Najeriya daga kasar Ingila

Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya dawo Najeriya.

A ranar Lahadi ne Tinubu ya dawo Najeriya daga kasar Birtaniya da misalin karfe 8 na dare.

Jirgin da ke dauke da shugaban jam’iyyar APC na kasa ya sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammed inda wasu shugabannin kungiyar yakin neman zaben sa suka tarbe shi.

Advertisement

Makonni kadan da suka gabata Tinubu ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Jim kadan bayan da ya yi tsokaci kan tsayawa takarar kujera ta daya, tsohon gwamnan jihar Legas ya tashi zuwa kasar Burtaniya.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa ya ce tafiyar tasa zuwa kasar Birtaniya na daga cikin dabarun yakin neman zabensa, inda ya ce yana tuntubar juna ne a kasar waje.

Advertisement