Al'umma

Yemi Osinbajo ya ziyarci Mahaifiyar marigayi shugaban ƙasa Ƴar’aduwa

An hangi mai girma Mataimakin Shugaban Tarayyar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo a gidan Mahaifiyar Marigayi tsohon shugaban kasa Alhaji Ummaru Muss Ƴar’aduwa, Hajiya Dada.

Advertisement

An bayyana cewa Mista Osinbajo da mukarrabansa sun je duba lafiyar ta ne.

Da take jawabi tun farko a yau, Hajiya Dada ta bayyana farin cikin ta da ziyarar tasa, sannan ta kuma yi kira gare shi da ya zama jagora nagari ga matasa.

Advertisement

Ta kuma yi addu’ar Allah Ta’ala Ya biya masa bukatun sa, Yasa shi cikin mafificin Shugaban kasa a Nijeriya bayan dan ta Marigayi Umaru Ƴar’aduwa.

A nasa jawabin, Mista Osinbajo ya gode mata bisa dukkan addu’o’in da ta yi masa, sannan ya kuma yi mata fatan kara tsawon rai don ganin yadda gwamnatinsa ke gudanar da ayyukanta.

Advertisement