Addini

Yaushe Za’a Fara Azumin Watan Ramadan Na 2023?

Yaushe ne Ramadan 2023? Mafarin sabuwar shekara yakan sa mutane su sa ido ga lokacin da Ramadan zai fara.

Ko da yake ainihin ranakun za su iya canzawa saboda ganin wata, amma ana sa ran za a fara watan Ramadan 2023 a ranar Alhamis 23 ga Maris, 2023. Wannan yana nufin cewa daren da ya gabata, ranar Laraba 22 ga Maris, 2023, zai zama farkon Taraweeh.

Ana sa ran kammala Ramadan a ranar Alhamis, 20 ga Afrilu, 2023, ma’ana Eid al-Fitr na iya fadowa a ranar Juma’a, 21 ga Afrilu, 2023.

Advertisement

Watan mafi tsarki

Ramadan shi ne wata na tara kuma mafi tsarki a cikin kalandar Hijira ta Musulunci kuma yana farawa ne idan aka ga jinjirin watan Ramadan.

Lokaci ya yi da za mu yawaita Ibada, yawaita Sadaqa da neman gafarar Allah (SWT).

Watan ne aka saukar da Alqur’ani ga Annabi (SAW).

Watan da kofofin Aljanna suke budewa, ana kulle kofofin wuta.

“Watan Ramadan (shi ne) wanda aka saukar da Alqur’ani a cikinsa, shiriya ga mutane, da hujjar shiriya da rarrabewa. To, wanda ya ga wata, to, ya azumce shi. Kuma wanda ya kasance majiyyaci ko kuwa a kan tafiya, to, daidai da adadin wasu kwanuka na dabam.

“Allah Yana nufin sauƙi a gare ku, kuma bã Ya nufin ku da tsanani, kuma Yana nufin ku cika lokaci, kuma ku yi tasbĩhi game da abin da Ya shiryar da ku.” Kuma tsammãnin ku, kunã gõdiya.”

Suratul Baqarah, aya ta 185

Advertisement