Tsaro

Yaron da aka kama da sunan suna taimakawa yan ta’adda a Gudun-Gudun ya kuɓuta

Idan za’a iya tunawa, Arewa Times Hausa kwanakin baya ta habarto cewa rundunar ta musamman da aka turo jihar Sakkwato domin fatattakar yan ta’addan dake addabar wasu yankunan jihar sun cafke gwamman mutanen da ake zargin suna taimakawa shugaban yan ta’addan Bello Turji Kachalla.

Advertisement

Rundunar wacce ta kunshi kwararrun jami’an tsaro daga cikin wadanda suak samu nasarar kamawa garin dake karamar hukumar mulki ta Illela har da wannan bawan Allah da kuke gani cikin hoton da aka bayyana sunan shi Mansur, wanda yayi rashin sa’a lokacin da yaje garin wajen bikin wani dan uwan shi kuma lokacin ne jami’an tsaron suka afka yankin wanda yayi kaurin suna game yan ta’adda da ake kyautata zaton Fulani ne.

Cikon Allah, kamar yadda muka bayyana kama shi wannan shafin, haka zalika a yau muke sake sanar da kubutar shi daga cikin wannan iftila’i da ya same shi bayan addu’o’i na jama’a.

Advertisement

Wani mai amfani da shafin Facebook a karamar hukumar Illela ne ya wallafa batun sakin nashi, wanda kuma mutane da dama suka tabbatar.

Advertisement