IlimiƘetare

Yaro Ɗan Shekara 10 Da Ya Cafki Nonon Malamar Su, Yayin Da Suka Rungume Juna

Wani yaro dan shekara goma da ke aji hudu a makarantar Holly Hill da ke gundumar Volusia a jihar Florida ta Amurka, an dakatar da shi saboda kama nonon malamar shi yayin da suka rungume juna.

Malamar ta yi ikirarin cewa yaron ya damke nonon ta na hagu a wulakance, sai da ta cire hannun shi.

Kakar yaron ta musanta zargin inda ta ce malamar ce ne ke da laifi domin ta rike hannun yaron kamar yadda jikan ta ya fada mata.

Advertisement

Jikan nata yace tare da rungumota ta kamo hannun shi ta rike fau, ita kuma bata san dalilin yin hakan ba. Yace ta bar hannun shi ya koma ya zauna ita kuma ta cigaba da magana da sauran dalibai.

Kakar ta amince da dakatarwar kwanaki goma na babban kamar yadda ta ce watakila hatsari ne.

‘Yan sanda sun shiga cikin lamarin dangane da cin mutuncin da ake zargin, kuma yaron zai fuskanci tuhuma kan laifin cin mutuncin, kamar yadda rahoton ‘yan sandan ya bayyana. Har yanzu dai ba a tuhume shi ba.

Yaron na iya fuskantar tuhuma kan laifin keta haddi na cin mutunci saboda rashin ɗa’ar shi wanda ya faru a ranar 24 ga Oktoba, 2022, lokacin da malamar a ziyarci aji don tattaunawa da su lokacin da yaron ya kai hannu don runguma.

Advertisement