Yariman Najeriya zai kwashe watanni 33 a gidan yarin Amurka akan damfara


Lauyan Amurka Brit Featherston dake gundumar Gabashin Texas ta sanar da yanke hukuncin daurin watanni 33 ga wani dan Najeriya, Sobanke Idris Sunday Adereti, a gidan yari na tarayya bisa samun shi da laifin damfara a gwamnatin tarayya.
Wata sanarwa da ofishin jakadancin Amurka da ke Najeriya ya fitar, ta bayyana cewa Adereti, mai shekaru 24, ya amsa laifin sji a ranar 25 ga Oktoba, 2021, na zamba da fasfo da yunkurin zamba a banki, kuma alkalin kotun Amurka Jeremy D ya yanke masa hukuncin daurin watanni 33 a gidan yari na tarayya, ranar Alhamis.
Dangane da takaddun kotu, a cikin watan Maris na shekarar 2021, Adereti ya gabatar da fasfo na karya da kuma takardar shaidar da aka sayo ta karya lokacin ƙoƙarin buɗe asusun banki a Flower Mound, Texas.