Tsaro

Yara 2 sun mutu a harin da Rasha ta kaiwuraren farar hula 33 a Ukraine – Hukuma

Kasar Rasha ta kai hare-hare kan wuraren farar hula 33 a cikin sa’o’i 24 da suka wuce, ma’aikatar harkokin cikin gida ta Kyiv ta sanar a ranar Juma’a yayin da sojojin Rasha suka mamaye babban birnin kasar, a cewar kamfanin dillancin labarai na Interfax.

“Rashawa sun ce basa harbin fararen hula. Amma a cikin sa’o’i 24 da suka gabata an kai hari kan wuraren farar hula 33,” inji wani jami’in ma’aikatar harkokin cikin gida ta Ukraine Vadym Denysenko.

Tun da farko, kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa an kashe yara biyu daga harin na Rasha, in ji wani jami’in ma’aikatar cikin gida ta Ukraine.

Advertisement
Advertisement