Tsaro

Yan tawaye sun kashe mutane 63 a DR Congo

Wasu ‘yan bindiga sun kashe akalla mutane 63 a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, in ji wata kungiyar agaji.

Kungiyar ta zargi mayakan CODECO da aikata kisan wanda ya faru da sanyin safiyar yau a sansanin Savo da ke kusa da Bule a lardin Ituri.

Kakakin rundunar sojin Ituri, Jules Ngongo, shi ma ya tabbatar da harin.

Advertisement

Sai dai ya yi ikirarin cewa mutane 20 ne suka mutu a harin.

Shugabar kungiyar agaji ta yankin Bahema-North Charite Banza Bavi, ta shaidawa manema labarai cewa mutane 40 ne suka samu munanan raunuka sakamakon harin.

Ya ce: “Dalibai biyu a makarantar da Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Norway ta tallafa suna cikin wadanda suka mutu. Maharan sun yi amfani da bindigogi da adduna.”

CODECO dai na daya daga cikin kungiyoyin ‘yan bindiga da ke gudanar da ayyukansu a gabashin Kongo a dai dai lokacin da ake fama da tashe tashen hankula kan filaye da albarkatun kasa.

Advertisement