Siyasa

Yan sandan Tunisiya sun kulle kofofin ofisoshin Majalisar Koli ta Shari’a

Yan sandan Tunisiya sun kulle kofofin majalisar koli ta shari’a da shugaba Kais Saied ya rusa a ranar Lahadi, tare da hana ma’aikatan shiga, kamar yadda shugaban majalisar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Litinin.

Sanarwar da Saied ya bayar ta haifar da fargaba ga bin doka da oda a Tunisiya bayan da ya kwace iko da kusan baki daya a bazarar da ta gabata a wani mataki da masu sukarsa suka kira juyin mulki, inda kungiyoyin alkalai ke zarginsa da wani haramtaccen aiki da ke zagon kasa ga ‘yancin shari’a.

Kungiyar alkalan kasar Tunisia ta fada jiya Lahadi cewa matakin da shugaban kasar Kais Saied ya dauka na rusa majalisar koli ta alkalan kasar da ke arewacin Afirka lamari ne mai hadari da ja da baya da ba a taba ganin irinsa ba daga nasarorin da kundin tsarin mulkin kasar ta samu.

Advertisement

Matakin da Saied ya dauka cikin dare shi ne mataki na baya-bayan nan na tabbatar da mulkin kasar bayan da ya kori majalisar dokokin kasar tare da korar firaministan kasar a watan Yuli, inda ya yi alkawarin sake fasalin kundin tsarin mulkin kasar Tunisia, wanda masu sukarsa suka kira juyin mulki.

Advertisement