Tsaro

Yan Sanda Sun Kashe Ɗan Bindiga 1, Sun Cafke Wasu A Kaduna

A wani farmakin da rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta kai kan ‘yan ta’adda da ‘yan daba, ta ce ta sake samun wata gagarumin nasara yayin da jami’an ta da ke aiki a sashin Rigachikun a ranar Asabar, 14 ga watan Janairu, 2023 suka kashe wani dan bindiga daya tare da raunata wasu da suka tsere da raunukan harbin bindiga.

Rundunar ‘yan sandan ta ce da misalin karfe 0100 na ranar Asabar, ta samu labarin cewa ‘yan bindiga sun kai farmaki gidan wani Umar Ibrahim da ke kauyen Amana Maimadachi da nufin yin munanan ayyukan su na ta’adanci.

Ya bayyana cewa da samun rahoton tashin hankalin, jami’an ‘yan sandan tare da sauran masu ruwa da tsaki a harkar tsaro sun yi gaggawar tashi zuwa wurin da suka yi artabu da ‘yan bindigar tare da dakile yunkurin su na yin garkuwa da ‘yan jihar masu bin doka da oda.

Advertisement

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Muhammad Jalige ya fitar, ya ci gaba da cewa, a farmakin da suka kai cikin dabara, an kashe daya daga cikin ‘yan fashin da ke sanye da kayan soja, yayin da wasu suka tsere da munanan raunukan harbin bindiga.

“An samu nasarar kwato bindiga kirar AK-47 dauke da harsashi guda hudu daga hannun ‘yan fashin da aka kashe,” in ji shi.

Advertisement