Labarai

Yan Sanda Sun Cafke Masu Garkuwa Da Mutane 3 A Abuja

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta cafke wasu masu garkuwa da mutane guda uku ‘yan mazauna Bwari tare da wasu mutane 13 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban tare da kwato manyan makamai da alburusai da suka hada da babba bindiga (GPMG).

Da yake gabatar da wadanda ake zargin da kuma makaman da aka kwato a ranar Asabar a hedikwatar rundunar, kakakin rundunar ‘yan sandan, Olumuyiwa Adejobi, ya ce kama su ya biyo bayan kaddamar da rundunar ‘yan sanda ta musamman (SIS) da Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP Kayode Egbetokun, ya yi, a matsayin wani gagarumin ci gaba wajen karfafa yanayin tsaro a babban birnin tarayya (FCT).

Rundunar ‘yan sandan ta ce, SIS ta yi aiki ne, ta hanyar hadin gwiwa da Hukumar Leken Asiri ta Force Intelligence – Intelligence Response Team (DFI-IRT), Sashen Yaki da Ta’addanci na FCT, Sashen Yaki da garkuwa da mutane da sauran su.

Adejobi, wanda ya bayyana sunayen masu garkuwa da mutane uku da ke yankin Bwari, dukkansu maza da “Idris Ishaku, Bala Umar da Dahiru Salisu dukkansu ‘yan shekara 27 ne” ya ce su ne ke da alhakin aikata jerin laifukan fashi da makami da garkuwa da mutane a karamar hukumar Bwari da sauran sassa na babban birnin tarayya Abuja.