Siyasa

Yan Najeriya da basu da katin zabe kwanaki 90 kafin ranar zabe ba za su iya kada kuri’a ba – Dokar Zabe

Yan Najeriya da suka rasa da katin zabe watanni uku gabanin ranar zabe ba su cancanci kada kuri’a ba, kamar yadda dokar zabe ta 2022 da aka yiwa kwaskwarima ta tanadar.

Kwanan nan ne shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) ya amince da kudurin dokar, bayan kin amincewa da farko kan wasu tanade-tanade da suka shafi zabukan fidda gwani na jam’iyyun siyasa.

Sai dai wadanda suka rasa da katunan su kuma suka nemi hukumar zabe mai zaman kanta za ta maye gurbin su bayan kwanaki 90.

Advertisement

Tun da farko dai an bukaci yan Najeriya da su nemi a kalla kwanaki 30 kafin zabe.

Advertisement