Siyasa

Yan majalisar dokokin Ukraine sun amince da sanya dokar ta-baci a fadin kasar

Yan majalisar dokoki a kasar Ukraine sun amince da kafa dokar ta baci a duk fadin kasar sakamakon fargabar mamayar Rasha.

Majalisar dokokin kasar ta amince da dokar shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy wadda ta sanya matakin na tsawon kwanaki 30 daga ranar Alhamis.

Dokar ta baci ta baiwa hukumomi damar sanya takunkumi kan zirga-zirga, toshe gangami da kuma haramta jam’iyyun siyasa da kungiyoyi “domin kare lafiyar kasa da zaman lafiyar jama’a.”

Advertisement

Matakin ya biyo bayan matakin da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya dauka jiya litinin na amincewa da yancin kai na yankunan yan tawaye a gabashin Ukraine, inda rikicin da aka kwashe kusan shekaru takwas ana yi da yayi sanadiyar mutuwar mutane sama da 14,000. Putin ya sanya takunkumin tura sojojin Rasha zuwa wurin don “wanzar da zaman lafiya” kuma ya sami amincewar majalisar dokoki don amfani da karfin soji a wajen kasar.

Hukumomin Ukraine sun sha bayyana damuwarsu kan cewa Rasha na iya kokarin kawo rudani a kasar ta hanyar dogaro da magoya bayan Moscow dake cikin kasar, ciki har da wata jam’iyyar siyasa mai goyon bayan Rasha da ke da wakilci a majalisar dokokin kasar.

Takardar ta kuma haramta “kayan bayanan da za su kawo cikas ga al’amura a kasar,” tare da baiwa gwamnati ‘yancin sanya dokar hana fita da kuma gudanar da bincike.

Advertisement