Al'umma

Yan kasar Morocco sun shiga cikin makoki bayan mutuwar wani yaro

An yi shiru mai ban tsoro a wani kauye na Morocco a ranar Lahadin da ta gabata bayan mutuwar wani yaro dan shekara biyar da ya makale a cikin rijiya tsawon kwanaki hudu.

Kwanaki – da dare – al’ummar Ighran, wani kauye a wani yanki mai tsaunuka a arewacin Maroko, sun taru a gefen rijiyar, suna murna da ma’aikatan ceto da masu aikin sa kai da ke tono wuri mai wahala don isa ramin da yaron Rayan, ya makale. Sun bayar da tallafi ga iyayen Rayan. Miliyoyin mutane ne suka kalli aikin ceton a gidan talabijin na kasar.

Masu aikin ceto ne suka fitar da yaron a daren ranar Asabar bayan wani dogon aiki da ya dauki hankulan duniya. Ganin cewa Rayan na raye, jama’a sun yi ta murna yayin da aka garzaya da yaron zuwa motar daukar marasa lafiya inda iyayensa ke jira.

Advertisement

‘Yan mintuna kadan bayan motar daukar marasa lafiya ta tashi, wata sanarwa daga fadar masarautar ta ce yaron ya mutu. Sarkin Morocco Mohammed VI ya bayyana ta’aziyyarsa ga iyayen yaron, Khaled Oram da Wassima Khersheesh.

Sakon goyon baya, damuwa da bakin ciki ga yaron da iyalansa sun taso daga sassa daban-daban na duniya yayin da labarin rasuwar Rayan ya bazu cikin daren jiya Asabar.

Fafaroma Francis a ranar Lahadin da ta gabata ya bayyana a matsayin “kyakkyawa” yadda mutane suka yi gangami a kokarin ceto rayuwar Rayan. Francis ya nuna godiya ga al’ummar Morocco a lokacin da yake gaisawa da jama’a a dandalin St. Peter’s Square. Ya yaba wa mutane saboda “sanya duk abin da suka yi” a kokarin ceto yaron.

Advertisement