Tsaro

Yan gudun hijira 368,000 sun tsere daga Ukraine tun bayan mamayar Rasha — MDD

Wani rahoto da hukumar kula da yan gudun hijira ta Amurka (UNHRC) ta fitar a yau Lahadi, ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, kimanin mutane 368,000 ne suka tsere daga kasar Ukraine zuwa kasashe makwabta, yayin da adadin yan gudun hijira ke cigaba da karuwa kwana guda bayan mamayar kasar da Rasha ta yi a kasar ranar Alhamis.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na twitter, hukumar ta UNHCR ta ce adadin na yanzu ya kai 368,000 kuma yana cigaba da karuwa.

Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta kuma lura cewa tsakanin Juma’a da Asabar, mutane 200,000 sun riga sun tsallaka kan iyakokin Ukraine a matsayin ‘yan gudun hijira.

Advertisement

“A ranar Asabar, adadin ya kai kusan mutane 150,000, in ji Filippo Grandi, kwamishinan ‘yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya yayin da yake tabbatar da rahoton.

Advertisement