Labarai

Yan Fashi Sun Kashe Wani Matashi, Suka Gudu Da Keken Napep A Suleja

‘Yan fashi sun gudu da Keken Napep din wani matashi bayan sun hallaka shi a Suleja dake jihar Naija.

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan fashi ne sun hallaka wani matashi mai suna Auwalu Muhammad, Dan asalin garin Gumel a jihar Jigawa, Najeriya, tare da guduwa da Keken Napep din da yake sana’ar achaba da shi.

Idris Aliyu (Bilili) wanda shine ubangidan matashin da ya rasa rayuwar shi wajen neman abinci, ya fadawa jaridar DDL Hausa cewa matashin ya dauki fasinjoji ne zuwa yankin Tapa a jihar Neja, inda suka shammace shi wajen yi masa mummunan rauni akan shi.

Haka zalika, an bayyana cewa an jima masa rauni a wani ɓangare na jikin shi tare da jan shi a kasa zuwa cikin daji, sannan suka daure shi da igiya da kuma kashe bayan da yayi yunkurin guduwa domin ya tsira da rayuwar shi.

Har zuwa lokacin kammala hada wannan rohoto dai, rundunar ‘yansandan jihar Neja bata ce komai ba game da afkuwar wannan lamari.