Labarai
Yan Daurin Aure Da Dama Sun Mutu Bayan Wata Yar Kunar Bakin Wake Ta Tayar Da Bam A Wurin
Ana cikin fargabar mutuwar mutane da dama a wajen wani daurin aure a ranar Asabar bayan da wata ‘yar kunar bakin wake ta tayar da bam a garin Gwoza na jihar Borno.
Wasu da dama kuma sun samu munanan raunuka a wurin daurin auren da ke Tashan Mararaba a cikin garin Gwoza.
Daya daga cikin wadanda suka tsira da ransu ya shaidawa manema labarai cewa ‘yar kunar bakin waken ta shiga wurin dauke da da jaririyar a bayanta sannan ta tayar da bam din.
Sai dai ba a tantance adadin wadanda suka mutu ba yayin da wadanda suka jikkata ke karbar kulawa a wani asibiti da ke garin.