Tsaro

Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 3, sun jikkata 1 a Zariya

A daren Lahadi ne wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka kai farmaki kauyen Rafinfa da ke Dembo a karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna inda suka yi garkuwa da mutane uku tare da harbe mutum daya.

Wani ganau mai suna Bala Zakari, ya shaida wa jaridar Blueprint cewa, “Wadanda aka yi garkuwa da su sun hada da Alhaji Ali Nura, Alhaji Lawal Musa, Alhaji Sahabi Rufa’i, yayin da Hudu Shuraihu kuma aka harbe shi a kirji kuma an garzaya da shi wurin kula da lafiya.”

Ayyukan garkuwa da mutane sun yi rauni a cikin Zariya da kewaye a cikin ‘yan kwanakin nan kafin lamarin ya faru a ranar Lahadi.

Advertisement

Mai martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmad Nuhu Bamalli, ya bukaci malaman addini da suka hada da Limamai da Fastoci da su yi addu’a kan rashin tsaro a Masarautar.

Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige, ya ci tura domin wayarsa ta kashe har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Lamarin dai ya zuwa yanzu an kashe mutane 13 a Kudancin Kaduna.

Advertisement