Tsaro

Yan bindiga sun tarwatsa kauyuka 8 a jihar Kebbi

Wasu yan bindiga sun kori kimanin mutane 15,000 mazauna kauyuka takwas da ke karamar hukumar Sakaba a masarautar Zuru ta jihar Kebbi.

Jaridar Blueprint ta tattaro cewa yan bindigar sun mamaye kauyukan ta hanyar amfani da gidajen da babu kowa a matsayin mafaka da kuma cin abincin da mazauna garin suka bari.

Kauyukan da yan bindigar suka mamaye a masarautar Makuku sun hada da Makuku, Doka, Jigawa, Mahuta, Kurmin Hudo, Bien, Sakaba da Maroro.

Advertisement

Masarautar Makuku da ke kudancin Masarautar Zuru tana da iyaka da jihar Neja tana da daji da tuddai wanda ke yiwa ‘yan fashin maboya da kuma hanyar shiga masarautar Yauri da ke makwabtaka da ita.

Wani mazauni al’ummar mai suna Alhaji Auwal Makuku yace “dole ne mu bar gidajen mu, mu nemi mafaka a wani wuri domin tsira. A kullum yan fashin suna tsoratar da mu, suna satar dabbobin mu, suna tarwatsa shagunan mu, suna fashin gidaje, suna kwashe duk wani abu mai amfani.”

“Rayuwa ta yi mana wuya a nan tunda ba sa barin mu mu je gonakinmu ba tare da yin wani kasuwanci ba,” in ji shi.

Ya kara da cewa al’ummar garin na da babbar kasuwa a Makuku da ake gudanarwa duk ranar Alhamis na mako amma hakan ya zama tarihi tun bayan da ‘yan fashin suka karbe iko da masarautar baki daya.

Alhaji Auwal ya ce, “har yanzu muna sansanin ‘yan gudun hijira da ke Dirin Daji, amma a wasu lokuta muna kai ziyara gidajen da ba kowa ba, domin mu debo kayan abinci, mu yi lale, kuma kafin mu yi haka sai mu hau kan tsaunuka don lura da motsinsu. ”

A cewar shi, an tanadi wasu rundunonin sojoji a kauyukan Ayyu da Dankolo, wanda hakan ya taimaka matuka wajen dakile yaduwar cutar, idan ba haka ba da sun isa garin Zuru a yanzu.

Advertisement