Tsaro

Yan Bindiga Sun Sace Daliban Makarantar Firamare A Nasarawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da sace wasu daliban makarantar firamare ta LGEA, Alwaza, al’ummar Alwaza, karamar hukumar Doma ta jihar a safiyar ranar Juma’a.

DSP Rahman Nansel, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce tuni rundunar hadin guiwa ta ‘yan sanda, sojoji da ’yan banga suka aike da wadanda suka yi garkuwa da su, inda aka ce suna kan babura.

Wata majiya ta kuma tabbatar wa manema labarai cewa harin ya faru ne da sanyin safiyar Juma’a.

Advertisement

Ya ce an tafi da wasu daliban firamare da ba a tantance adadin su ba a harin bayan da rahotanni suka ce ‘yan bindigar sun yi wa yaran kawanya a lokacin da yaran ke zuwa makaranta.

Ya ce har yanzu ba a san inda daliban da wadanda suka sace su suke ba amma kuma ya tabbatar da cewa an aike da jami’an tsaro domin ganin an kubutar da daliban daga hannun wadanda suka sace su lafiya.

Advertisement