Yan Bindiga Sun Kewaye Masallacin Juma’a, Sun Kashe Masu Ibada A Kaduna
A ranar Juma’ar da ta gabata ne ‘yan bindigar suka kai hari a wani masallaci da ke Angwar Makera, a unguwar Kwasakwasa a karamar hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna, inda suka kashe mutum biyu.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 2 na rana a lokacin sallar Juma’a.
Hudu Kwasakwasa, shugaban al’ummar yankin, wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, ya ce ‘yan bindigar sun bude wuta kan masu ibada.
“Masu ibada biyun da aka kashe na daga cikin musulmin da aka kai wa hari a masallacin Juma’a na Angwar Makera a lokacin da ‘yan bindigan suka bude musu wuta tare da sace wasu a yau.
An binne wadanda abin ya shafa a makabartar tsohon Kuyello,” inji shi.
A cewarsa, mutanen suna cikin raka’a na biyu na sallah a lokacin da aka kai musu hari, lamarin da ya tilasta wa sauran mutanen tserewa domin tsira da rayukansu.
Ya kara da cewa a kwanakin baya, ‘yan fashin sun yi awon gaba da mutane kusan 9 a wata unguwa da ake kira Angwar Kanawa da ke karkashin yankin Kwasakwasa.
A baya an rahoto cewa sabon harin ya faru ne sa’o’i 24 bayan ‘yan bindigar sun sace dalibai sama da 287 a karamar hukumar Chikun dake makwabtaka da jihar.
Da DAILY POST ta tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan ya ce yana cikin wani taron tsaro.
Sai kawai ya ce, “A halin yanzu muna taron tsaro, idan mun gama zan kai muku da rahoton.