Tsaro

Yan Bindiga Sun Kashe Wani Kansila

Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun kashe kansila mai wakiltar mazabar Allawa a karamar hukumar Shiroro a jihar, Mista Saleh Yakubu, kamar yadda jami’in gwamnati ya tabbatar.

Kwamishinan tsaro na cikin gida da ayyukan jin kai, Mista Emmanuel Umar, ya ce ya samu labarin cewa an kashe kansila a hanyar shi ta zuwa Allawa.

Ya ce har yanzu cikakkun bayanai game da kisan nasa ba su da tushe.

Advertisement

Umar ya ce ana zargin mamacin da wani mutum guda a kan babur ne ‘yan ta’addan suka tare su.

Ya ce an nemi marigayin ya sauko daga kan babur ne ‘yan ta’addan suka bude masa wuta.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan, Mista Abiodun Waisu, ya ce har yanzu rundunar ba ta samu labarin faruwar lamarin ba.

Amma Mista Daniel Jagaba, shugaban ma’aikatan shugaban karamar hukumar Shiroro, Akilu Kuta, ya ce ya samu kiran wayar tarho daga shugaban karamar hukumar inda ya shaida masa cewa kansilan ya bar garin Kuta zuwa mahaifarsa garin Allawa a karshen mako kuma an kashe shi.

Daga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya

Advertisement