Tsaro

Yan bindiga sun kashe mutum daya a filin jirgin sama a Kaduna

A ranar Asabar din da ta gabata ne yan bindiga suka kashe mutum daya a wani hari da suka kai a filin jirgin sama a jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida na jihar, Mista Samuel Aruwan, wanda ya tabbatar da faruwar harin a wata sanarwa da ya fitar a Kaduna, ya ce wanda abin ya shafa ma’aikaci ne a filin jirgin.

Ya kara da cewa an harbe wanda aka kashen ne bayan da yayi ihun ganin yan bindigar.

Advertisement

Aruwan yace: “Duk da haka, sojojin da ke ciki da wajen filin jirgin sun mayar da martani tare da fatattakar maharan.

“Aikin tashar jirgin ya koma tare da shirin tashi da saukar jiragen sama bayan faruwar lamarin.

“Jami’an tsaro na gudanar da ayyuka a babban filin jirgin. Za a sanar da ƙarin bayani ga jama’a.”

Advertisement