Siyasa

Yan bindiga sun kashe mutane, sun lalata rumfunan zabe a Enugu

Wasu yan bindiga sun kashe mutane uku a zaben kananan hukumomin da aka yi ranar Laraba a jihar Enugu.

Wasu shaidun gani da ido sun shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun far wa rumfunan zabe biyu da ke Obeagu ward III a Enugu ta Kudu a cikin babura inda suka fara harbe-harbe kai tsaye.

Biyu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, an same su ne da harsasan feshi.

Advertisement

Daga bisani sun zarce zuwa wata rumfar zabe a Akpugo, karamar hukumar Nkanu ta Gabas yayin da ake ci gaba da kada kuri’a tare da kawo cikas ga aikin.

Daga bisani sun zarce zuwa wata rumfar zabe a Akpugo, karamar hukumar Nkanu ta Gabas yayin da ake ci gaba da kada kuri’a tare da kawo cikas ga aikin.

Yan bindigar sun kuma lalata rumfunan zabe yayin da wasu mutane suka tsere da saran adduna.

Advertisement