Tsaro

Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 11 da wasu mutane a Niger

Yan bindiga sun kashe akalla mutane 30 ciki har da jami’an tsaro a wasu hare-haren da suka kai a jihar Neja a makon jiya.

Yan ta’addan sun kai hari a Galadiman Kogo da wasu al’ummomi a kananan hukumomin Shiroro da Paikoro a ranar Juma’a da Asabar, inda suka kona gine-gine tare da kwashe kayan abinci.

Gwamnan jihar, Abubakar Bello, wanda ya tabbatar da harin a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Mary Noel-Berje ya fitar ranar Talata, ya ce jami’an tsaro 11 ne suka mutu a hare-haren.

Advertisement

Ya kara da cewa an kuma kashe yan bindiga da dama a hare-haren.

Bello ya ce: “Masu aikata laifukan da suka haura sama da 100 sun mamaye al’ummomin da rana tsaka, sun kashe jami’an tsaro na hadin gwiwa 11, mazauna kauyuka da dama, tare da jikkata da dama.

“Gwamnatin jihar ta riga ta samu oda da izinin shugaban kasa Muhammadu Buhari na gudanar da ayyukan soji a yankin da abin ya shafa a kokarin fatattakar ‘yan ta’adda.

“Hakika mun daina hakuri da ‘yan ta’adda kuma za mu yi amfani da duk wata hanya mai yiwuwa don kawo karshen wadannan hare-hare na zubar da jini a kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba. Za mu yi duk mai yiwuwa don dakatar da kashe-kashen da kuma dawo da al’ummar da abin ya shafa.”

Advertisement