Tsaro

Yan Bindiga Sun Harba Makamin Roka Cikin Wani Garin Zamfara

Wasu ‘yan bindiga a ranar Talata sun harba makamin roka zuwa garin Birnin Magaji, hedikwatar karamar hukumar Birnin Magaji a jihar Zamfara, kamar yadda jaridar Daily Trust ta tattaro.

Karamar hukumar Birnin Magaji tana da iyaka da karamar hukumar Batsari mai fama da rikici a jihar Katsina.

Karamar hukumar dai ta kasance wurin da ‘yan bindigar ke kai hare-hare da yaran Dankarami da wani Ardo Nashawari.

Advertisement

Wani shugaban ’yan banga da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Daily Trust cewa tun da farko wasu ’yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan wasu manoma da ke aikin gonakin su mai nisan kilomita gabas da garin.

“Yayin da manoman suka yi nasarar tserewa ba tare da an samu korafe-korafe ba, sai ga ’yan banga namu da suka yi fice suka shirya tare da bin su, nan take fadan ya barke, bayan da suka samu labarin cewa ‘yan banga ba za su yi kasa a gwiwa ba a yakin da suke yi, sai ‘yan ta’addan suka nemi agaji.

“Wasu gungun mutane dauke da makamai ne a kan babura suka fito suka fara jefa gurneti a wajen mu, gurnetin da aka harba ya bata inda aka nufa, a kusa da wani rafi daya daga cikin su ya fashe ya haifar da wani katon rami.

“A harin da aka kai babu wanda ya rasa ransa ko kuma ya jikkata, sannan an tilasta wa maharan tserewa, mu ‘yan banga mun mayar da al’adarmu mu yi wa kanmu makamai tare da tabbatar da tsaron garinmu tunda mun san cewa ‘yan bindiga na iya kai hari a kowane lokaci.

Advertisement