Siyasa

Yakin Rasha da Ukraine: Zelenskyy ya nemi Putin a yi tattauna kai tsaye

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya bukaci takwaran shi na Rasha Vladimir Putin da ya zauna domin tattaunawa kai tsaye tare da kawo karshen mamayar da Rasha ke yiwa kasar shi, yayin da ya kuma yi kira ga kasashen Yamma da su kara tallafin soji ga Kyiv (Ukraine).

Da yake magana da manema labarai a ofishin shi da aka killace a babban birnin Ukraine, Zelenskyy a ranar Alhamis ya gargadi kasashen yammacin duniya cewa Rasha za ta iya zuwa sauran kasashen Turai idan harin sojan Putin yayi nasara a Ukraine.

“Ba wai ina son yin magana da Putin ba,” in ji shugaban na Ukraine. “Ina bukatan magana da Putin. Duniya na bukatar tattaunawa da Putin. Babu wata hanya da za’a iya dakatar da wannan yakin.

Advertisement

Sa’an nan, da yake magana akan Putin, yace: “Me kuke so daga gare mu? Ku bar ƙasar mu.”

Ya kara da cewa, “Ku zauna tare da ni, ba nisan mita 30 ba,” in ji shi, yana mai nuni ga Putin ya karbi shugabannin duniya a wani babban teburi mai tsayi.

Putin ya kaddamar da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine a makon da ya gabata, yana mai bayyana shi a matsayin “aikin soji na musamman” da nufin kawar da “neo-Nazis” da ke mulkin kasar.

Advertisement