Kimiyya

Yadda Za’a Yi Amfani Da Shafin Sada Zumunta Na “Twitter” A Ko Ina (Hotuna)

Idan dai mai karatu bai manta ba, watanni kimanin biyar da suka wuce Gwamnatin Najeriya ta haramta ayyukan kamfanin sada zumunta na Twitter a faɗin ƙasar ga baki daya.

Gwamnatin Najeriya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta bayyana cewa wadansu bata gari na amfanin da dandalin wajen tunzura jama’a da ingiza tashin hankali wanda ka iya kai ga asarar rayuka, kamar yanda gwamnatin ta buga misali da zanga-zangar “ENDSARS” wacce ta barke a watannin baya, musamman a jihar Legas.

Zanga-zangar “ENDSARS” ta haddasa asarar rayuka da duniyoyin miliyoyin Naira a fadin Najeriya, cikin har da mutuwar jami’an tsaro.

Advertisement

Dalili kuma na gaba wajen haramta Twitter a Najeriya shine; kamfanin ya goge wani sakon Shugaban kasa Buhari wanda aka yi ta cece-kuce akai kai kafin rufe Twitter.

Saboda haka a yau zamu nunawa masu karatu hanya mafi sauki ta amfani da Twitter akan wayoyin ku na Android.

Abu daya da zaku yi shine; ku sauke, ko kuyi downloading na wannan “Application” akan google play store, sannan ku bude kuyi “Connecting”.

Idan kuka yi “Connecting”, application din zai nuna muku “Connected”.

Kun yi nasara, sai shiga shafin na Twitter.

Mun gode. Turawa sauran mutane wannan Post, babbar kulawa ce.

Advertisement