Yadda Za’a Magance Matsalar Ciwon Haƙori Cikin Sauƙi

Mene ne ke kawo ciwon haƙora? Sannan kuma ya za’a magance matsalolin da suka shafi haƙora da magungunan gargajiya?

Ciwon hakori ko ciwon hakora yana faruwa ne lokacin da jijiya a tushen hakori ko kewayen haƙori ta samu wani akasi.

Ciwon hakori (Toothache) a turance, shine lalacewa, rauni, ko asarar hakori sune mafi yawan abubuwan da ke haifar da ciwon hakora.

Yadda za’a magance matsalolin ciwon haƙora a sauƙaƙe;

Domin magance matsalolin da suka shafi ciwon haƙori, abu biyu ne kawai ake bukata kamar yanda zamu bayyana a yau.

1. Man Kanumfari (Clove Oil);

2. Garin Kanumfari (Clove Powder);

Yanda za’a sarrafa wadannan kayayyakin na gargajiya;

Idan hakori yana ciwo, ko gyangyadi tare da ciwo mai tsanani, abin da za’a yi shine a samu tsabtataccen auduga (Cutton), sai a dan diga man kanumfari dan madaidaici akan ausugar, sai a makala a wurin da abin ya shafa na tsawon mintuna 15.

Za’a yi hakan safe da yamma, musamman lokacin shiga barci.

Idan kuma hakorin sun yi rami, sai a gwaɓa man da garin na kanumfari a juya sosai. Bayan sun garwayu da kyau, sai a diba a makala cikin ramin idan za’a shiga barci.

Da safe kuma a sake yin hakan har tsawon sati daya.

Inshaa’Allah da yardar Ubangiji za’a samu saukin wannan mstsalar.

Da fatan za’a turawa sauran yan uwa domin su amfana.….