Wasanni

Yadda tsohon Gwamnan Sokoto na farko, Shehu Kangiwa ya rasu a wajen wasa

Muhammadu Shehu Kangiwa shine zababben gwamnan jihar Sokoto na farko. An zabe shi a ofis a watan Oktoban 1979 a jamhuriya ta biyu mai kankanin lokaci. Ya mutu a watan Nuwamba 1981 lokacin da ya fado daga kan doki yayin da yake buga wasan polo a gasar Jojiya. Ya rasu yana da shekara 28 a duniya.

Duk da cewa gwamnatinsa ta kasance ta ɗan gajeren tarihi na tunawa da shi a matsayin gwamna wanda ya yi tasiri sosai a rayuwar al’ummarsa. An ce ya gina otal-otal, irin su Giginya Hotel, wanda ya kasance daya daga cikin mafi kyau a kasar a zamaninsa, don karfafa kasuwanci a jihar. Ya kuma kiyaye tsarin ilimi kyauta ga yan asalin jihar, tare da littafan karatu da riguna kyauta a matsayin hanyar bunkasa ilimi a tsakanin al’ummarsa.

Polo wasan dawakai ne, wasan filaye na gargajiya, kuma daya daga cikin tsoffin wasannin qungiyar da aka fi sani a duniya. Kungiyoyi biyu masu hamayya da juna ne ke buga wasan da nufin zura kwallo ta hanyar amfani da mallet na katako mai tsayin hannu don buga wata karamar kwallo mai karfi ta cikin ragar kungiyar. Tawagar wasan polo ta ƙunshi ‘yan wasa huɗu.

Advertisement
Advertisement