Al'umma

Yadda Pele Ya Taimaka Wajen Kawo Karshen Yaƙin Biyafa A 1967 Zuwa 1970

Fitaccen dan wasan wanda cikakken sunansa Edson Arantes do Nascimento ya yi tattaki zuwa Najeriya ne a watan Janairun 1969 tare da kungiyarsa ta Santos ta Brazil domin buga wasan sada zumunci da Super Eagles, wadanda a da ake kira Green Eagles a lokacin. A wannan lokacin Najeriya na cikin yakin basasa.

Saboda karfin tuwo da ba da umarni na babban dan wasan kwallon kafa, bangarorin da ke fada da juna sun yanke shawarar kawo karshen yakin na tsawon sa’o’i 48 domin su kalli wasannin sada zumunta guda biyu. An buga wasan farko ne a Legas, kuma aka buga na biyu a Benin.

A ranar 26 ga Janairu, 1969, tawagar Brazil ta isa a tsakiyar yakin, a shirye don buga wasa da Green Eagles a Legas. Wasan ya gudana ne a Najeriya. Pele ne ya ci wa Brazil kwallayen biyu a wasansu da Santos, inda aka tashi kunnen doki da ci 2-2.

A ranar 4 ga Fabrairun 1969 ne aka sake buga wani wasan baje koli tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Brazil da kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, a jihar Bendel da ke kasar Benin a lokacin da kungiyar ta Brazil ta kai ziyara can. Samuel Ogbemudia wanda ke rike da mukamin Gwamnan Soja na jihar a lokacin ya yi shelar hutu tare da kula da bude gadar da ta hada Benin da Biafra.

A lokacin an ce akwai magoya bayansa kusan 25,000 a cikin filin wasan domin shaida wasan mai cike da tarihi wanda Pele ya jagoranci tawagarsa ta doke Najeriya da ci 2-1. Edu da Negreiros ne suka zura wa Santos kwallayen, sannan Okere ya ci wa kungiyar ta Midwest kwallon a ragar kungiyar.

An sake dawo da aika-aika ne kusan nan da nan bayan da tawagar ta bar Najeriya.

Pele ya koma Najeriya ne a ranar 26 ga Afrilu, 1978, domin halartar wasan sada zumunci da wata tawagar Brazil mai suna Fluminese. An buga wasan ne da Racca Rovers a filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna. Pele ya kasance a filin wasa kawai na mintuna 45.

Air Commodore Dan Suleiman, wanda yake rike da mukamin Gwamnan Jihar Filato a lokacin, ya karrama shi ne ta hanyar sanya masa suturar gargajiya ta Filato da Babban Riga da na Zannah.

Credit Photo Google