Labarai

Yadda Boko Haram Ta Yaudari Kungiyar ISWAP Da Sunan Sulhu Inda Suka Kashe Ƴan ISWAP 56

A wani labarin da jaridar Leadership Online ta wallafa a yammacin jiya, an ruwaito cewa wasu fusatattun mayakan Boko-Haram, sun kashe matan ‘yan ta’addar Daesh 33 a dajin Sambisa, domin daukar fansar kisan da aka yi musu na kwamandan su Malam Aboubakar (Munzir) da wasu 15 da aka kashe a wani kazamin fada da ‘yan ta’addar ISWAP suka yi.

Bayanin da aka bayar ya bayyana cewa tun ranar 3 ga watan Disamba, 2022, wani babban jigo na kungiyar Boko-Haram mai kula da tsaunin Mandara, wanda aka bayyana sunan shi da Ali Ngulde, ya jagoranci daruruwan mayakan shi wajen kaddamar da yaki da ‘yan ta’addar ISWAP a Sambisa.

Yadda Fadan Ya Fara…

Leadership ta ruwaito cewa, wadannan hare-haren sun fara ne bayan rashin tattaunawar da kungiyar ‘yan ta’adda ta Jama’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād (bangar Boko-Haram) suka fara, yayin da suka gayyaci mayakan na ISWAP zaman sulhu, tare da yin alkawarin mika kan su (mubayi’a) ga shugabancin ISWAP.

Advertisement

Mayakan na ISWAP ashe ba su sani ba cewa Ngulde da tawagar su sun yi musu kwanton bauna (domin daukar fansa ga ‘yan Boko-Haram da mayakan ISWAP suka kashe a baya), inda aka kashe akalla 12 daga cikin mayakan na ISWAP a Yuwe da harbin bindiga, yayin da wasu kuma sun iya tserewa da raunukan harsasai.

Bayan harin kwantan bauna, ‘yan ta’addar Boko-Haram sun kwace wasu Motoci kirar Hilux guda hudu wadanda aka jibge su da makaman abokan hamayyar su tare da kona wata guda.

Wata majiya mai tushe ta ce, jim kadan bayan nasarar Boko-Haram, sun tattara karin mayaka daga sansanoni daban-daban domin kai wa wasu mayakan ISWAP hari a garuruwan Ukuba, Arra da Sabil Huda da Farisu, inda suka kashe karin mayaka kusan 23 da mata 33.

Advertisement