Kannywood
Trending

Yadda Bidiyon Maryam Yahaya da Minal Ahmad Rungume da Juna Suna Rawa Ya Janyo Cece-Kuce

Fitattun jaruman masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood Maryam Yahaya,Minal Ahmad da kuma dayar wato Momee Gombe ayanzu haka suna Kasar Dubai suna shakatawa.

Ayanzu haka ana kiyastin cewa tun zuwansu Dubai dai ayanzu zasu iya shafe kimanin kusan wata daya Kenan da Zuwa.

Ba yau ne Yan Kannywood musamman mata suka fara zuwa kasar Dubai ba yawon bude ido da kuma shakatawa ba, saidai wasu idan sukaje cham din, suna barin abun Fadi da Cece-Kuce.

Bama kasar Dubai ba kadai, jarumai mata da maza na kannywood kanje garuruwa daban daban yawon shakatawa. Saidai sunfi Zuwa Dubai din.

Ti a wannan Karon ma ansamu Wasu jarumai mata su biyu da suka janyo cece kuce kamar dai yadda aka Saba da zarar wani Dan Kannywood yake Dubai.

Wannan al’amari yafaru ne acikin satinnan da Maryam Yahaya tareda Minal Ahmad Suka saki wani bidiyonsu a Tiktok suna rwa da waka rugume da Juna.

Kalli bidiyon ⬇️

Hakan ta zama ala’ada kokuma nace ala’ada idan har sukaje kasar waje, sukan yi bidiyo da kuma daukan Zafafan Hotuna idan sunje. Saidai akan samu wasu daga cikinsu dakeyin Abunda bai dace ba.

Back to top button